Zargin badaƙalar Naira 4.6: Kotun tarayya ta bayar da belin kwamishinan kudi na jihar Bauchi

Yakubu Adamu (1)

Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, wanda ke fuskantar shari’a kan zargin hannu a badaƙalar Naira biliyan 4.6.

Alkalin shari’ar, Emeka Nwite, ya amince da bayar da belin ne a kan kudi Naira miliyan 500 tare da mutane biyu masu tsaya masa a adadin kudi iri daya, inda kotun ta ce dole ne masu tsayawar su kasance masu kadarorin fili a yankunan Asokoro, Maitama ko Gwarinpa na babban birnin tarayya Abuja tare da shaidar mallaka da za a iya tantancewa.

Kotun ta kuma umarci masu tsayawar belin da su gabatar da rantsuwar bayanin karfin kudi, tare da umurtar wanda ake tuhuma ya mika fasfo dinsa na tafiya kasashen waje, ta yadda ba zai fita daga kasar nan ba sai da izinin kotu.

An kuma sanya ranar fara sauraron shari’ar gaba daya, yayin da kotun ta jaddada cewa laifuffukan da ake zargi a kan wadanda ake tuhuma na daga cikin laifukan da doka ta amince a bayar da beli a kansu.

Karin labari: Zargin badaƙalar Naira Biliyan 4.6: kotu ta tsare kwamishinan kudi na jihar Bauchi

Tun da farko, hukumar EFCC ta gurfanar da Yakubu Adamu, wanda tsohon manajan reshen bankin Polaris ne a jihar Bauchi, kan tuhume-tuhume shida na wankiyar kudade, tare da hada kamfanoni biyu, Ayab Agro Products da Freight Company Limited, a matsayin wadanda ake tuhuma a shari’ar.

Hukumar ta bayyana cewa an karkatar da kudaden da aka ware domin samar da babura, inda duk da cewa ba a aiwatar da kwangilar ba, an raba kudaden zuwa hannun mutane da kamfanoni daban-daban duk da sanin cewa kudaden sun samo asali ne daga haramtacciyar hanya.

Kotun ta kuma bayyana cewa kwamishinan zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje har sai an yanke hukunci kan wata shari’a ta daban da ta shafi zargin daukar nauyin ta’addanci da ke rataye a kansa, yayin da binciken EFCC ya danganta karkatar da kudaden da wani lamunin bankin Polaris da aka ce gwamnatin jihar Bauchi ce ta bayar da garantinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here