Rundunar ‘yan sanda ta jihar Lagos ta ayyana fitaccen mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin tayar da hankalin jama’a da kuma shirya zanga-zangar da ta haifar da toshe manyan hanyoyi a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mashood Olohundare Jimoh, ne ya bayyana hakan, inda ya ce, an kama mutane goma sha uku da ake zargi da hannu a ɓarna da rashin zaman lafiya bayan rushe gidaje a unguwar Oworonsoki da ke Lagos.
Jimoh ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo barazana ga tsaron jama’a ba, musamman a yankin gadar Third Mainland da ke da muhimmanci ga tattalin arzikin birnin.
Ya kuma ce an tura jami’an tsaro a manyan sassa daban-daban na jihar domin hana masu zanga-zanga toshe hanya da jawo cunkoson ababen hawa.
Kwamishinan ya nanata cewa duk wanda aka kama yana ƙoƙarin tayar da hankalin jama’a za a kama shi, a bincike shi kuma a gurfanar da shi gaban kotu.
Ya ƙara da cewa jihar Lagos ita ce zuciyar tattalin arzikin Najeriya, don haka hukumomi ba za su yarda da duk wani abu da zai kawo rikici ko cikas ga rayuwar al’umma ba.













































