Shugaban majalisar wakilai, Dr. Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa majalisar tana goyon bayan shirin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na amfani da kuɗaɗen aro wajen gudanar da manyan ayyukan raya al’umma.
Abbas ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron ƙungiyar cibiyoyin kasafin kuɗi na majalisun dokoki na Afirka (AN-PBO) da aka gudanar a Abuja.
Ya ce duk da cewa a baya kalamansa sun jawo fassarar da ba daidai ba, ba wai ya yi adawa da aro gaba ɗaya ba, sai dai yana kira da a yi amfani da shi cikin tsari da gaskiya.
Ya jaddada cewa aro a kasashe na zamani ana amfani da shi ne wajen gina muhimman abubuwa kamar wutar lantarki, hanyoyi da noma, wanda zai ƙara samar da kuɗaɗen shiga da rage talauci, ba wai a karkatar da shi zuwa cin hanci da rashawa ba.
Abbas ya ce majalisar ta 10 ta tabbatar da cewa aro mai tsari da gaskiya muhimmin kayan aiki ne wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma kare marasa galihu.
Karanta: 2025: Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 4.32 cikin ɗari a zango na biyu na shekara
Abbas ya kuma bayyana cewa talauci har yanzu yana ƙarauwa a nahiyar Afirka, inda sama da mutane miliyan 464 ke rayuwa cikin matsanancin talauci a shekarar 2024.
Ya ce matsalar rashin aikin yi, musamman ga matasa, na kara tabarbarewa yayin da ake samun sababbin matasa miliyan 12 a kasuwar aiki kowace shekara, amma aikin da ake samarwa bai wuce miliyan uku ba.
Ya kuma nuna damuwa kan asarar kuɗaɗe ta hanyar cin hanci, fitar kuɗin haram, da gazawar tsare-tsare, inda ya ce Afirka na asarar sama da dala biliyan 587 a kowace shekara.
A cewarsa, waɗannan kuɗaɗen da ake rasa su ne ya kamata a yi amfani da su wajen gina asibitoci, makarantu da hanyoyi a nahiyar.
Abbas ya ce majalisar na ƙara faɗaɗa aikin sa ido, binciken lissafin kuɗi da kuma ƙarfafa dokokin yaƙi da cin hanci.
Ya bayyana cewa ana sake fasalin dokar kula da kasafin kuɗi da kuma dokar saye-saye na gwamnati domin rufe guraben da ake amfani da su wajen satar kuɗi.
Haka kuma, hukumar yaƙi da cin hanci na samun ƙarin ƙarfin aiki domin dakile asarar kuɗaɗe da ake kiyasta ya kai kashi huɗu cikin ɗari na GDP na ƙasar.
Ya ƙara da cewa don magance matsalolin kuɗi da shugabanci, majalisun dokoki na Afirka dole su rungumi sabbin fasahohi kamar na’urar fasaha ta zamani AI, domin su inganta tsare-tsare da bincike.
Ya kawo misalai daga ƙasashen Estonia da Koriya ta Kudu, inda amfani da fasahar zamani ya taimaka wajen rage asarar kuɗaɗe da tabbatar da gaskiya a harkokin gwamnati.
NAN













































