Wata gobara da ta tashi da safiyar Juma’a ta lalata kusan shaguna 50 a Kasuwar Fatima Simra Mai Hada-hadar Kayayyaki da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano.
Lamarin na zuwa ne kasa da mako guda bayan wata babbar gobara ta shafi sama da ’yan kasuwa 1,500 a Kasuwar Singer.
A cewar shugaban kwamitin gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula, gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 5:40 na safe a ranar Juma’a.
Ya ce shagunan da abin ya fi shafa su ne ƙananan sana’o’i da ke harkar sarrafa mai da sake sarrafa robobi da leda.
Chula ya ce gobarar na ci gaba da ƙamari har sai da jami’an kashe gobara suka iso wurin, yayin da ’yan kasuwa suka nuna damuwa kan jinkirin zuwan jami’an.
Har yanzu ba a tantance girman asarar da aka yi ko ko akwai asarar rayuka ba.
Wannan shi ne karo na uku cikin ’yan makonni da gobara ke lalata kasuwa a Kano, lamarin da ke ƙara jefa ’yan kasuwa cikin mawuyacin hali.
Lamarin ya sake zama wani mummunan koma baya ga harkokin kasuwanci a Kano bayan gobarar Kasuwar Singer da ta lalata dukiyoyi ta Biliyoyin Naira.










































