NDC ta sanya miliyan 60 kudin fom din shugaban kasa, ta fitar da jadawalin zaben fidda gwani

NDC NDC

Jam’iyyar ND ta sanya Naira miliyan 60 a matsayin jimillar kudin da ‘yan takara za su biya domin neman tikitin shugaban kasa a gabanin zaben 2027.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Shugabanta na kasa, Sanata Moses Cleopas, da Sakatare Ikenna Enekweizu suka fitar a ranar Talata a Abuja.

“Kudin da aka amince da shi da ‘yan takar shugaban kasa za su biya Naira miliyan 20 na Fom din Nuna Sha’awa, sai kuma Naira miliyan 40 na Fom din Takara.

Yan takar gwamna za su biya Naira miliyan 10 na Fom din Nuna Sha’awa da Naira miliyan 20 na Fom din Takara.

Sanarwar ta kuma ce, ‘yan takar majalisar dattawa, an sanya kudi Naira miliyan 3 da Naira miliyan 5, yayin da ‘yan takar majalisar wakilai za su biya Naira miliyan 2 da Naira miliyan 4.

Ta kuma bayyana cewa ‘yan takar majalisun jihohi za su biya Naira miliyan 1 na Fom din Nuna Sha’awa da Naira miliyan 1.5 na Takara.

Sai dai jam’iyyar ta ce ta bai wa mata da nakasassu rangwame, inda za su biya kashi 50 cikin 100 da kashi 25 cikin 100 a kowane mataki.

NDC ta kuma fitar da jadawalin siyar da Fom din Nuna Sha’awa da na Takara, tantance ‘yan takara da gudanar da zaben fidda gwani.

A cewar jadawalin, siyar da Fom din Nuna Sha’awa zai fara ne a ranar 13 ga Mayu ya kare a ranar 18 ga Mayun, yayin da tantancewa da tattaunawa da ‘yan takara za a yi daga 19 zuwa 21 ga Mayu.

Jam’iyyar ta ce siyar da fom din takara za ta fara nan da nan bayan tantancewar daga 21 zuwa 23 ga Mayu, tana mai cewa dole ne a mika fom din da aka cika a ranar 25 ga Mayu ko kafin haka.

Ta bayyana cewa za a saurari korafe-korafen da suka taso daga tantancewar a ranar 25 da 26 ga Mayu, yayin da zaben fidda gwani na mukamai daban-daban za a gudanar a ranar 27 da 28 ga Mayu.

Zaben fidda gwani na Shugaban Kasa, a cewar jam’iyyar, an tsara shi ne a ranar 29 ga Mayu a Abuja.

NDC ta bayyana cewa za a tantance ‘yan takar majalisun jihohi a jihohinsu, yayin da tantancewar ‘yan takar majalisar kasa da na shugaban kasa za a yi a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Ta kuma bayyana cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na gwamna a matakin kananan hukumomi.

Jam’iyyar ta ce za a bukaci duk ‘yan takara su sanya hannu kan alkawari bisa ka’idodinta da dabi’a.

Ta kara da cewa jam’iyyar za ta yi amfani da tsarin yin zabe a bayyane domin tabbatar da gaskiya, adalci da dimokuradiyya ta cikin gida.

Ta sake jaddada aniyarta ta gudanar da zaben fidda gwani mai cike da gaskiya da adalci wanda zai samar da ‘yan takara masu kwarewa a zaben 2027. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here