Tinubu zai tafi Afrika ta Kudu da Angola a ranar Laraba

Tinubu depart US 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai bar Abuja a ranar Laraba domin ziyarar kasashe biyu, wato Johannesburg da ke South Africa da kuma Luanda da ke Angola.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, zuwansa na farko zai kasance taron koli na shugabannin ƙasashe na G-20, sannan daga nan ya wuce Angola domin taron ƙungiyar Tarayyar Afrika AU da kungiyar Tarayyar Turai EU.

Tinubu ya samu gayyata daga shugaban South Africa Cyril Ramaphosa wanda ke shugabantar ƙungiyar G-20 a bana.

A shekarar 2024 ma, lokacin Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil ya jagoranci G-20, ya gayyaci Shugaba Tinubu zuwa taron Rio de Janeiro.

Taron na Johannesburg za a yi shi daga 22 zuwa 23 ga Nuwamba, inda shugabannin manyan ƙasashe 20 na duniya da EU da AU da cibiyoyin kuɗi za su tattauna kan batutuwan ci gaban tattalin arziƙi da sauyin yanayi da tsare-tsaren abinci da makamashi.

Taron ya kasance ƙarƙashin taken “Hadin kai, Daidaito, Ɗorewa” kuma ya ƙunshi zaman tattaunawa kan bunkasa cigaba mai ɗorewa da rage gibin tattalin arziƙi, da rawar kasuwanci, da hanyoyin sauƙaƙa bashin ƙasashe masu tasowa.

Haka kuma za a tattauna batun sauyin yanayi, kare lafiyar al’umma daga annoba, tsare-tsaren makamashi na adalci da tsarin samar da abinci da kalubalen hakar ma’adanai da ci gaban fasaha, musamman Artificial Intelligence.

A yayin taron, Shugaba Tinubu zai gudanar da tattaunawa domin inganta manufofin Sabunta Fata “Renewed Hope” da kuma tattauna batutuwan zaman lafiya da tsaro da cigaban tattalin arziƙi.

Bayan kammala taron G-20, Shugaban Najeriya zai bi sahun sauran shugabannin AU da EU zuwa taron haɗin guiwa na ƙungiyoyin biyu da za a gudanar a Luanda daga 24 zuwa 25 ga Nuwamba.

Taron na AU da EU zai haɗa matasa shugabanni, masu kirkire-kirkire da kungiyoyin farar hula domin tattauna kalubalen da suke fuskanta tare da samar da hanyoyin magance su, musamman a fannonin sauyin yanayi, cigaban tattalin arziƙi, ababen more rayuwa, fasahar intanet, masana’antar kirkire-kirkire, sarrafa kayayyaki da kuma aikin noma.

Shugaban zai yi tafiyar ne tare da ministoci, masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Yusuf Tuggar, Ministan Kuɗi Wale Edun, Ministan Ma’adanai Dele Alake, Ministan Harkokin Kasuwanci Jumoke Oduwole da Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa Mohammed Mohammed.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala tarukan biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here