Majalisar Dattawa a ranar Talata ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin jami’an soja 100,000 domin ƙara ƙarfin yaƙi da ta’addanci, fashi da makami da kuma magance yawan sace ’yan makaranta da ke ƙara kamari a sassan ƙasar nan.
Majalisar ta kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan Shirye-shiryen Kare Makarantu, tana tambayar yadda kuɗaɗen da aka ware don shirin kyautata tsaro ke zirarewa amma ana ci gaba da kawo wa makarantu hari.
Damuwa ta ƙaru ne bayan harin da aka kai Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata a Maga da ke Jihar Kebbi, inda ’yan bindiga suka kashe mataimakin shugabar makarantar tare da sace ɗalibai 25.
Tattaunawar ta biyo bayan ƙarin buƙatu daga Sanata Adams Oshiomhole na Edo ta Arewa a zaman majalisar, lamarin da ya tayar da mahawara kan tabarbarewar tsaro a ƙasar nan.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya jagoranci zaman, inda daga bisani aka shiga zaman sirri domin tattauna bayanai na cikin gida kan tsaro.
Sanata Oshiomhole yayin gabatar da buƙatar ƙarin ɗaukar sojoji da kuma sake tantance tsarin tsaro ya jaddada cewa girman matsalar tsaro na buƙatar faɗaɗa rundunonin sojoji da gaggawa.
Ya kuma nemi a binciki kuɗaɗen da aka ware wa Shirye-shiryen Kare Makarantu tare da ƙara fasahar zamani a aikin jami’an tsaro.
Majalisar ta amince da buƙatar ne gaba ɗaya, yayin da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya goyi bayan ƙarin ɗaukar sojoji 100,000 tare da gudanar da bincike kan kuɗaɗen shirin kare makarantu, yana mai gargadin kauce wa siyasantar da batun tsaro.
Sannan ya mika ta’aziyya ga waɗanda abin ya shafa a harin makarantar Maga.













































