An yi jana’izar jarumin wasan Hausa Sani SK

2A314C22 BCB0 4483 BE89 4C1AA6375FC3
2A314C22 BCB0 4483 BE89 4C1AA6375FC3

A safiyar yau alhamis aka gudanar da jana’izar jarumin wasan Hausa Sani SK a unguwar ‘yar Mai Maishinkafi dake cikin birnin Kano.

A yammacin jiya laraba ne Sani Garba SK ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke unguwar Nasarawa a cikin birnin Kano.

A baya dai an sha yada jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa da kansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here