FRSC: Hatsarin mota ya ragu da kashi 12.8% a cikin watanni goma

Accident road 700x430

 

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta sanar da raguwar hatsarin mota da kashi 12.8% daga watan Janairu zuwa Oktoba 2024 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2023.

Shugaban FRSC, Malam Shehu Mohammed, ya bayyana hakan a Abuja, yana mai cewa wannan ci gaba ya samo asali ne daga kokarin hukumar na inganta tsaron hanya.

Mohammed ya ce adadin hatsarurrukan ya ragu daga 8,654 a 2023 zuwa 7,675 a 2024, yayin da yawan mutanen da suka jikkata ko suka mutu ya ragu da kashi 2.5%.

Sai dai ya ce adadin mutuwar ya karu saboda manyan hatsarurruka, kamar na Jigawa da Minna.

Ya kara da cewa hukumar na aiki don cimma burin rage yawan mutuwa a kan hanya da kashi 5% duk shekara, tare da hadin gwiwar al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.

Hakanan, FRSC na gudanar da kamfen din wayar da kai don ilmantar da direbobi game da mahimmancin bin dokokin hanya.

Mohammed ya jaddada bukatar goyon bayan jama’a domin rage hatsarurrukan mota da tabbatar da tsaro a hanyoyin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here