Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) reshen jihar Kano ta zargi Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na Rudunar ‘Yan Sandan Jihar Kano da tsoratar da daya daga cikin mambobinta, Mustapha Abubakar Adam, Esq., bayan kama shi da tsare shi, ta kuma yi kira ga lauyoyi da su halarci kotu don nuna goyon baya gare shi.
Ana cikin wata sanarwa da Sabon Shugaban NBA na Kano, Sani Ammani, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana lamarin a matsayin hari kan lauyoyi kuma ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta fafata da abin da ya kira ‘tsoratar da jami’ai’ ga mambobinta.
A cewar sanarwar, an tsare Adam a ranar Talata, 30 ga Yuni, bisa umarnin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka na rudunar na Jihar Kano, bayan da ya kalubalanci abin da jami’in ofishin, saboda hana shi shiga domin kare mutumin da yake karewa, duk da jira kusan minti 40 yayin da aka bar wasu mutane, ciki har da bangaren da ke adawa da shi, su ka shiga.
Kungiyar ta ce laifin Adam kawai shi ne bayyana abin da aka yi masa da ‘Na rashin dacewa’, yana mai cewa an sake shi cikin dare bayan da shugabannin kungiyar sun shiga cikin lamarin.
Sanarwar ta kara da cewa shugabannin NBA na Kano da Ungogo sun gana da Kwamishinan ‘Yan Sanda da DC na CID a ranar 1 ga Yuli domin warware lamarin cikin lumana.
A yayin tattaunawar, an ce DC na CID ya yarda cewa ya dauki matakin ne bisa shawarar jami’in kula da bangaren na (OC Legal), wanda ya fassara amfani da kalmar ‘Rashin dacewa’ da Adam ya yi a matsayin cin mutuncin jami’in ‘yan sanda.
Ko da yake taron ya kare da alamar sulhu, kungiyar ta zargi cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda da DC na CID daga baya sun sauya matsayarsu ta hanyar cewa dole ne lauyan ya rubuta takardar neman gafara.
“NBA ta Kano ba za ta mika kai ga tsoratar jami’ai ba,” in ji Ammani.
Ya bayyana cewa kungiyar ta taimaka wa Adam samun umarnin kotu da ke hana ‘yan sanda kama shi akan wannan lamari.
Shugaban ya kuma ce kungiyar ta samu ingantaccen bayani cewa ‘yan sanda sun gaggauta shigar da Rahoton Bayanan Farko FIR a kan lauyan kuma sun kira shi ya bayyana a gaban Kotun Majistare Mai Lamba 54 da ke Gyadi Gyadi a Kano, a ranar Juma’a.
“Hari kan lauya daya a yayin aikinsa, hari ne kan daukacin lauyoyi. Ba za mu nade hannu mu bari a aikata laifi ko a tsoratar da mambobinmu akan aikinsu ba,” in ji Ammani.
Ya yi kira ga mambobin kungiyar da su halarci shari’ar a kotu da yawa don nuna goyon baya ga abokin aikinsu da kare mutuncin lauyoyi.













































