Tsararru 52 sun fara rubuta jarrabawar NECO da NABAIS a gidajen gyaran hali da ke Kano

IMG 20260703 WA0056 750x430

Tsararru 52 a gidajen gyaran hali a fadin Jihar Kano sun fara rubuta jarrabawar kammala Sakandare ta (SSC) ta shekarar 2026 da Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO) da ta Ilimin Larabci da Nazarin Musulunci (NABAIS) ke gudanarwa, yayin da Hukumar Gyaran Hali ta Kasa (NCoS) ke ci gaba da fadada damammakin ilimi da nufin sake gyara dabi’un tsararrun.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, shiyar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce gudanar da jarrabawar na nuni da jajircewar hukumar wajen sake gyara, daibaita halayya da kuma samun nasarar mayar da tsararrun cikin al’umma ta hanyar ba su damar samun ilimi da bunkasa kwarewa.

A cewar sanarwar, masu rubuta jarrabawar sun hada da maza 41 da mata 11 da aka fito da su daga gidajen gyaran hali daban-daban a fadin Jihar Kano.

SolaceBase ta ruwaito cewa Kwamandan cibiyoyin Kula da Gidajen Gyaran Hali na Kano, Yusuf Ahmad Lakpene, ya sanya ido kan fara jarrabawar a wuraren da aka ware, inda ya bayyana wannan aikin a matsayin wani gagarumin ci gaba cikin aikin gyara da saisaita dabi’un tsararru.

Da yake jawabi ga masu rubuta jarrabawar, Lakpene ya bukace su da su nuna da’a da ladabi da rikon amana a tsawon lokacin rubuta jarrabawar, yana mai cewa ilimi na daga cikin hanyoyi mafiya inganci na sauya rayuwa da shirya masu tsare don rayuwa bayan zaman gidan gyaran hali.

“Ilmi na daga cikin hanyoyi mafiya inganci na sauya rayuwa, rage komawa aikata laifi da kuma shirya tsararru don sake dawowa cikin al’umma cikin nasara bayan kammala wa’adin zamansu a gidan gyaran hali,” in ji shi.

Mai kula da gidajen gyaran halin ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan daukar nauyin kudin yin rajistar tsararrun, inda ya ce wannan tallafi na nuna jajircewar gwamnatin a kan ilimi.

Ya kara da cewa baiwa tsararru damar samun ilimi na nuna kudirin gwamnatin na bunkasa harkar da ta shafi rayuwar dan adama ba tare da barin wani bangare a baya ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here