Kano ta cimma gagarumar nasara a bangaren samar da ruwa yayin da matatar Challawa ta fara fitar da tataccen ruwa

FB IMG 1783002253468 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta samu wani gagarumin ci gaba a kokarinta na dawo da samar da ruwa a fadin jihar, bayan samun nasarar fitar tataccen ruwa daga matatar ruwa ta Challawa zuwa ma’adar ruwa ta Goron Dutse.

Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahiru M. Hashim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Laraba bayan ya kai ziyarar duba aikin dawo da samar da ruwa da kuma duba wasu sassa na layukan ruwan da ke rarraba ruwan.

A cewar kwamishinan, tawagar dubawar ta shaida yadda aka samu nasarar tura ruwan da aka tsaftace daga matatr Ruwan ta Challawa zuwa Goron Dutse, inda ya bayyana ci gaban a matsayin wani babban mataki na inganta samar da ruwa ga mazaunan Jihar Kano.

“Wannan wani muhimmin ci gaba ne a kokarinmu na dawo da samar da ruwa a fadin Jihar Kano,” in ji Hashim.

Ya bayyana cewa idan an kammala gyaran ma’adar ruwan Goron Dutse, zai iya adana har zuwa lita miliyan 40 na ruwan da aka tsaftace, wanda zai inganta rarraba ruwa a fadin birnin Kano da kewaye.

Hashim ya kara da cewa ana ci gaba da gyara gaba daya matatar ruwan Challawa, wadda ke samar da kashi 51 cikin 100 na Ruwan da ake bukata a Kano gaba daya, domin dawo da ita ta ci gaba da aiki cikakke.

SolaceBase ta ce gyaran matatar ruwan Challawa wani bangare ne na kokarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi don farfado da harkar ruwa a fadin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here