Cibiyar kare hakkin jama’a ta Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) ta yabawa gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebolo, bisa gaggarumin matakin da ya dauka biyo bayan wani mummunan kashe-kashe da aka yi wa matafiya a Uromi, Jihar Edo, a ranar 27 ga Maris, 2025.
Wadanda aka kashen ‘yan asalin karamar hukumar Bankure ne da ke jihar Kano, sun fuskanci kisan gilla a hannun wata kungiyar ’yan banga da ke aikin tsaro na jihar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan CISLAC, Kwamared Auwal Musa Rafsanjani, kungiyar ta bayyana goyon bayanta ga yadda Gwamna Okpebholo ya dauki nauyin gudanar da wannan mataki.
SolaceBase ta ruwaito cewa gwamnan ba wai ya ziyarci iyalan wadanda suka rasu a jihar Kano ne kawai don jajantawa ba, har ma ya ba su tabbacin yin adalci.
Bugu da kari, Gwamna Okpebholo ya sanar da dakatar da dukkan kungiyoyin ‘yan banga a jihar Edo nan take tare da dakatar da kwamandan jami’an tsaro na jihar Edo, CP Friday Ibadin mai ritaya, bayan da aka bayyana cewa kungiyar ‘yan banga da ke da alhakin kisan gillar na gudanar da ayyukan ta ba bisa ka’ida ba.
Karanta har ila yau: Kisan Uromi: Zan biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa – Gwamna Okpebolo
Kungiyar ta yabawa gwamnan kan yadda yi tsayuwar daka wajen tabbatar da cewa dukkanin kungiyoyin tsaro suna gudanar da ayyukansu bisa ka’idojin doka, ta yadda za a samar da muhallin da ake baiwa ‘yan kasa hakkinsu.
CISLAC ta kuma yaba da kudurin Gwamna Okpebholo na tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da iyalansu, yana mai jaddada cewa za a kama wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su gaban kuliya.
Ana kuma jinjinawa hadin gwiwar gwamnatocin Edo da na jihar Kano a matsayin abin koyi ga sauran shugabannin Najeriya, wanda ke nuna muhimmancin hadin kai, tausayi da jajircewar jagoranci a lokutan bala’i.
Kungiyar ta kuma yabawa al’ummar jihar Edo musamman mazauna garin Uromi da suka sadaukar da rayukansu domin ceto wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa.