Bam ya kashe mutane 8 tare da raunata 21, yayin da Zulum ke jajantawa wadanda abin ya shafa

Babagana Zulum 750x430

Gwamnan Borno Babagana Zulum, ya jajantawa wadanda harin bom da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne suka dasa a hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Fashewar ta haddasa mutuwar mutane takwas tare da jikkata wasu 21 a ranar Asabar, daidai lokacin da Motocin mutanen ke tafiya a kan babbar hanya.

Sha hudu daga cikin wadanda suka jikkata sun samu munanan raunuka, yayin da wasu bakwai kuma aka yi musu jinyar kananan raunuka a asibitin kwararru na jihar dake Maiduguri.

Zulum, wanda ya ziyarci wadanda abin ya shafa, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, musamman yadda Borno ba ta fuskanci harin bam a cikin sama da shekara guda ba.

Karin karatu: NDLEA ta lalata haramtattun kwayoyi masu nauyin kilo miliyan 1.6

Zulum ya bayyana alhininsa game da asarar rayuka tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan. Ya kuma jaddada aniyarsa na tallafawa sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro.

Ya kuma yi alkawarin inganta tsarin tsaro na cikin gida, ciki har da tallafawa rundunar hadin gwiwa ta farar hula (CJTF) da kuma matasa masu sa kai da ke da hannu a ayyukan yaki da ta’addanci.

Gwamnatin jihar ta yi kira da a kara yin hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin leken asiri na cikin gida da hukumomin tsaro don inganta tsarin tsaro da kuma hana kai hare-hare nan gaba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here