NDLEA ta lalata haramtattun kwayoyi masu nauyin kilo miliyan 1.6

WhatsApp Image 2025 04 12 at 13.36.21 750x430

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta lalata tarin miyagun kwayoyi masu nauyin kilogiram miliyan 1.6 na haramtattun abubuwa da aka kama a fadin jihohin Legas da Ogun da kuma Oyo, wanda ya zuwa yanzu sune mafi girman muggan kwayoyi da za a kona a cikin nasarorin da hukumar ta samu.

SolaceBase ta ruwaito cewa an gudanar da bikin ƙone su a bainar jama’a da wakilan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai, sauran hukumomin tsaro, abokan huldar kasa da kasa, kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin al’umma, da dai sauransu.

Kuma an gudanar da shi ne a wani kebabben wuri a Ipara, kan hanyar Legas zuwa Ibadan, jihar Ogun, a ranar Asabar, 12 ga Afrilu, 2025.

Wata sanarwa da Femi Babafemi, Daraktan Hukumar NDLEA ba sashin yada labarai da wayar da kai a Abuja ya fitar a ranar Asabar, ta ce wasu haramtattun kwayoyi da aka lalata sun hada da hodar ibilis mai nauyin kilo 123; 46.8 kilogiram na tabar heroin; kilogiram miliyan 1.4 na cannabis; kilogiram 148,000 na syrup codeine; kilogiram 3,244.26 na tramadol; kilogiram 1,544 na skuchies; da kilogiram 111 na methamphetamine, da sauransu.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ya ce, wannan aiki shaida ce ta jajircewar hukumar wajen magance matsalar safarar miyagun kwayoyi a kasar nan.

Ya gargadi ga masu safarar muggan kwayoyi da cewa zamani ya canza kuma ba za a samu wurin numfashi ko wata mafaka a Najeriya ba, domin kuwa hukumar ta NDLEA, ta shirya tsaf don cimma burinta na hukunta wadanda suka saba wa doka.

Ya ce, a cikin shekaru hudu da suka gabata, mun samu nasarar gurfanar da masu aikata laifuka 10,572 tare da hukunta su, wadanda a yanzu haka suke zaman gidan yari daban-daban.”

Shugaban hukumar ta NDLEA wanda ya samu wakilcin daraktan kula da kadarori da binciken kudi na hukumar (DAFI), Dr. Ibrahim Abdul, ya bada hujjar lalata haramtattun magungunan da aka kwace a bainar jama’a da cewa don nuna gaskiya da riƙon amana, kuma wannan darasi ne.

A nasa jawabin a wajen bikin, gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaro, AIG Olusola Subair mai ritaya ya yabawa kokarin shugabanni da jami’an hukumar ta NDLEA bisa jajircewa, kwarewa, kokarin da suke yi na dakile miyagun kwayoyi kafin su kai ga al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here