Gwamnatin tarayya ta ce furucin da yan majalisar wakilai na Arewa-maso-Gabas suka yi na cewa an cire shiyyar gaba daya daga shirin noma da kiwo (SAPZ) ba gaskiya ba ne.
Sanata Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Abuja, yayin da yake mayar da martani ga sanarwar yan majalisar wakilai na Arewa-maso-gabas.
Kyari ya ce kungiyar, a cikin wata sanarwa, ta ce an cire Arewa maso Gabas gaba daya daga shirin SAPZ.
SAPZ wani bangare ne na tsare-tsare na gwamnatin tarayya da nufin bunkasa masana’antar noma, kuma manufar shirin shi ne sanya kowa da kowa a cikin sa.
Ya ce an kaddamar da shirin SAPZ ne a shekarar 2022 bisa la’akari da tsarin sa na mataki na 1 a shekarar 2019.
Ya bayyana cewa, bayan da suka karbi bayyaninsu, wata tawaga ta hadin gwiwa da ta kunshi ma’aikatar noma ta tarayya, ma’aikatar kudi ta tarayya, bankin raya kasashen Afirka, sun gudanar da wata ziyara zuwa kowace jiha domin tabbatar da cika sharuddan cancanta a matsayin tsarin shirin.
Kyari ya ci gaba da bayanin cewa SAPZ shiri ne na rancen wanda ke nufin gwamnatin tarayya ta hau kan bashin da aka samu ga jihar don aiwatar da shirin.
Ministan ya ce tuni aka fara kashi na biyu na shirin da gaske.
Kyari ya bayyana kwarin gwiwar cewa karin Jihohi za su yi abin da ake bukata don cika ka’idojin cancanta don baiwa gwamnati damar sanya su a cikin tallafin kashi na biyu.
Ya ce bayan shirin na SAPZ, gwamnatin yarayya za ta ci gaba da bayar da tallafi ga manoman Arewa maso Gabas da ma fadin kasar nan.(NAN)