Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mafarauta 16 da aka kashe.
Wasu gungun ‘yan banga ne suka kashe su a Uromin jihar Edo, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kano.
Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da tare da takwaransa na Jihar Kano Abba Yusuf, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mafarauta a Torankawa da ke Jihar Kano.
“Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa,” in ji shi.
Labari mai alaƙa: A biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, sannan a hukunta masu laifi – NBA ga gwamnan Edo
Okpebholo ya yabawa al’ummar jihar Kano kan yadda suka kwantar da hankalinsu duk da halin da ake ciki.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu.
“Muna tabbatar muku da cewa za a gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kuliya.
“Na yi alkawarin kudi da kayan abinci ga iyalan wadanda abin ya shafa,” in ji shi.
Ya kuma yi alkawarin cewa za a biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi adalci ga wadanda abin ya shafa. (NAN)