A biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, sannan a hukunta masu laifi – NBA ga gwamnan Edo

WhatsApp Image 2025 03 31 at 17.02.18 (1)

Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) reshen Kano ta yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu ‘yan asalin Kano 16 a jihar Edo, inda ta yi kira da a yi adalci da bin doka da oda daga hukumomi.

Shugaban hukumar NBA reshen Kano, Usman Umar Fari ya bayyana hakan a ranar Litinin, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan aiki da bai kamata a bar shi haka ba.

A cewar sanarwar, wadanda abin ya shafa na komawa Kano ne yayin da jami’an hukumar tsaro ta ESSC a jihar Edo, wacce a da aka fi sani da ESSN suka tare su a Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa, a ranar 27 ga Maris, 2025.

Jami’an tsaron sun yi zargin cewa ‘yan Boko Haram ne, inda suka yi musu mugun duka, tare da kona su.

Karanta har ila yau: Kisan Edo: Gwamna Okpebolo ya ziyarci Kano yayin da Gwamna Yusuf ke neman diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa

Wadanda suka tsira daga harin sun shaida cewa jami’an ne suktma yi kisan, lamarin da ya bayyana a matsayin kisan gilla.

Ya kuma ba da tabbacin hukumar ta NBA reshen Kano za ta sa ido sosai kan lamarin, inda ya kara da cewa, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin shari’a idan ba a yi adalci ba, dole ne a kare hakkin dan Adam na wadanda abin ya shafa.

SolaceBase ta ruwaito da yake jajantawa, ya ce, “Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan da gwamnati, da al’ummar jihar Kano, muna kuma jajantawa wadanda suka jikkata, muna kuma yi musu addu’ar samun lafiya cikin gaggawa.

Kisan dai ya janyo cece-ku-ce, inda da dama suka yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa domin ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here