Kisan Edo: Gwamna Okpebolo ya ziyarci Kano yayin da Gwamna Yusuf ke neman diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa

WhatsApp Image 2025 03 31 at 16.23.04 720x430

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebolo, ya kai ziyarar jaje ga gwamnatin jihar Kano da iyalan mafarauta 16 da wasu mutane suka kone kurmus a garin Uromi na jihar Edo. 

Da yake magana a gidan gwamnati a ranar Litinin, Okpebolo ya bayyana kaduwarsa kan lamarin tare da ba da tabbacin cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan.

SolaceBase ta ruwaito cewa gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa za a yi adalci ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Karanta: Kisan Uromi: Gwamna Okpebolo ya gana da Sanata Barau kan kisan yan Arewa a Edo

Hakazalika, Gwamna Yusuf ya yabawa gwamnan Edo kan matakin da ya dauka cikin gaggawa na magance matsalar tsaro bayan harin, sai dai bukaci a tabbatar an hukunta masu laifin.

Gwamna Yusuf ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bayyana sunan mutanen da kuma fuskokinsu.

Bugu da kari, ya bukaci Gwamna Okpebolo da ya tabbatar an biya diyya ga iyalan wadanda suka mutu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here