Kisan Uromi: Gwamna Okpebolo ya gana da Sanata Barau kan kisan yan Arewa a Edo

WhatsApp Image 2025 03 31 at 14.46.45 750x430

Za mu tabbatar an gurfanar da masu laifin – Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya kai ziyarar jaje ga mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin bisa kasan gillar da aka yi wa matafiya yan Kano a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

Ganawar ta su ta kasance a gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa a Abuja ranar Litinin.

SolaceBase ta ruwaito cewa wasu gungun mutane sun damke matafiyan da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Kano don gudanar da bukukuwan Sallah, inda suka yi awon gaba da motarsu, tare da yi musu kisan gilla a ranar Alhamis, wanda rahotanni suka tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa mafarauta ne daga jihar Kano.

Karin karatu: Kungiyar lauyoyi NBA Ungogo ta bukaci a hukunta wadanda suka kashe matafiya 16 ‘yan Arewa a Edo

Mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban majalisar dattawa kan harkokin yada labarai Alhaji Ismail Mudashir, ya ce gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga mataimakin shugaban majalisar wanda ya fito daga jihar Kano, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Gwamnan jihar Edo ya bayyana cewa mutane 14 da aka kama wadanda ake zargi da hannu a kashe matafiya da ba su ji ba ba su gani ba, za a kai su Abuja domin ci gaba da yi musu tambayoyi.

Yayin da yake tabbatar da cewa wadanda suka aikata laifin za su fuskanci fushin doka, ya bayyana kisan a matsayin abin takaici da Allah wadai.

Da yake mayar da martani, mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce dole ne a gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su zama darasi ga wasu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here