Kungiyar lauyoyi NBA Ungogo ta bukaci a hukunta wadanda suka kashe matafiya 16 ‘yan Arewa a Edo

WhatsApp Image 2025 03 31 at 10.37.26 1 750x430

Kungiyar lauyoyin Najeriya NBA reshen Ungogo a jihar Kano, ta yi kakkausar suka tare da neman a yi masu adalci kan kisan da aka yi wa matafiya 16 ‘yan arewa a jihar Edo, tare da bayyana lamarin a matsayin babban take hakkin dan Adam. 

A wata sanarwa da shugaban reshen, Ahmad A. Gwadabe ya fitar a ranar Litinin, ya nuna matukar damuwarsa kan lamarin, inda ya ce abin takaici ne kuma ba za a amince da shi ba.

Gwadabe ya kara da cewa, “Mun yi matukar kaduwa da damuwa matuka game da kisan da aka yi wa matafiya da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ke wucewa ta cikin jihar kawai, wannan matakin ya saba wa ka’idojin mutuntaka,” in ji Gwadabe.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Edo da jami’an tsaro da su gaggauta binciki lamarin tare da tabbatar da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya.

Karin karatu: Cikin Hotuna: Sarki Sanusi ya bukaci a hukunta wadanda suka kashe ’yan asalin Kano a Edo, ya bukaci matasa su guji daukar fansa

SolaceBase ta ruwaito cewa kungiyar ta kuma bukaci gwamnati da ta bayar da diyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da aiwatar da matakan hana afkuwar irin haka nan gaba.

Sanarwar ta karkare da yin kira da a kwantar da hankula, inda ta bukaci iyalan wadanda abin ya shafa da su kasance masu bin doka da oda wajen neman adalci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here