Labari da dumi-dumi: Kotu Ta Bada belin Dakataccen Akanta-Janar

images 5 4 1 710x430 1
images 5 4 1 710x430 1

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Babban Akanta Janar na Tarayya, Idris Ahmed tare da wadanda ake tuhumar su bisa sharuddan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC ta bayar.

 Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Adeyemi Ajayi ya ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba, kuma idan sun so sai su nemi izinin kotu ko kuma a soke belinsu.

Kotun ta kuma bayyana cewa wadanda ake tuhumar za su rattaba hannu kan yarjejeniyar cewa za su bi ka’idojin belin da EFCC ta gindaya musu.

Mai shari’a Ajayi ya kuma ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar kada su sayi fasfo na daban ba har sai an kammala shari’ar, bayan sun ajiye fasfo dinsu na asali ga hukumar.

Alkalin kotun ya zatar da hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba.

Alkalin kotun ya zatar da hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba. Kotun ta kuma bayyana cewa, bisa tsarin doka, wadanda ake tuhumar suna da damar bayar da belinsu duk da zargin da ake musu, tun da mai gabatar da kara bai bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun aikata ba daidai ba a lokacin da suke hannun EFCC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here