Sakamakon Tsarin Tantance takardun daukar aiki da ofishin hukumar daukar Ma’aikata na gwamnatin tarayya ya gudanar, an gano ma’aikata dubu 3 da 657 da suka gaza kawo shaidar takardar daukar aiki.
Hakan dai na nuna cewa, sun shiga aikin ne ta bayan gida, dalilin da yasa hukumar ta tura su zuwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC domin su fuskaci hukunci.

Shugabar Hukumar, Folashade Yemi-Esan wadda ta bayyana hakan ta ce, hukumar samu nasarar ceto gwamnati daga sulalewar kudi har Naira Miliyan 180 a kowane wata.
Adadin da ya kai Naira biliyan 2 a kowace shekara nan.













































