Yau Alhamis ne ake sa ran wata babbar kotun jihar Kano a arewacin Najeriya za ta yanke hukunci bisa kisan da aka yi wa wata karamar yarinya Hanifa Abubakar.
Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Dasambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.
Kisan nata ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, suka yi tur da shi.
Bayanai sun tabbatar da cewa wasu mutane ne suka ɗauke ta a babur mai kafa uku da ake kira A-Daidaita-Sahu bayan ta dawo daga makaranta a kan hanyarta ta zuwa gida inda suka tafi da ita.













































