Tinubu zai buɗe taron shekara-shekara na Editoci a Abuja

Bola Tinubu scaled 1 750x430 (1)

Kungiyar Editocin Najeriya (NGE) ta sanar cewa za ta gudanar da taron shekara-shekara na 2025, wanda ake kira da taron ɗaukacin editocin Najeriya (ANEC) daga ranar 3 zuwa 6 ga Nuwamba a Abuja.

A cewar sanarwar da shugabanta, Eze Anaba, tare da sakataren kungiyar, Onuoha Ukeh, suka rattaba wa hannu, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne zai buɗe taron.

Taken taron na bana shi ne “Mulkin Dimokuraɗiyya da Haɗin Kan Ƙasa, da kuma Matsayin Editoci.”

Karin karatu: Mamallakin jaridar PRNigeria ya kai NIPSS ƙara kan janye shi daga samun horon SEC 47 ba bisa ka’ida ba

Sanarwar ta bayyana cewa za a tattauna kan ƙalubale da damar da ke fuskantar editoci wajen inganta dimokuraɗiyya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Haka kuma, za a yi bitar yadda editoci za su iya amfani da dabaru da hanyoyin da suka fi dacewa wajen kare darajar ƙasa da haɗa kan al’umma.

Bisa ga bayanin kungiyar, shugaban ƙasa, shugabannin jam’iyyun adawa da manyan ‘yan siyasa sun sha jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen haɗa kan al’ummomin Najeriya masu bambancin addini, kabila da siyasa.

Kungiyar ta ce a daidai lokacin da ake fama da matsalolin tattalin arziki, akwai buƙatar ƙarfafa haɗin kai, musayar ra’ayi da haɗin gwiwa domin tabbatar da daidaito a ƙasar.

Za a gudanar da bikin buɗe taron a rana ta farko, tare da halartar shugaban ƙasa Tinubu, Ministan Babban Birnin Tarayya, Barista Nyesom Wike, Ministan Yaɗa Labarai da Ƙyautata Hangen Nesa, Alhaji Mohammed Idris, gwamnoni, jakadu, da ‘yan kasuwa daga sassan ƙasa da ƙetare.

Haka kuma, za a gabatar da muhimman takardu da jawabai, ciki har da “Rigimar Zaɓe da Amincin Kotuna,” “Halin Ƙasa: Buƙatar Sauye-sauyen Siyasa da Tattalin Arziki,” da kuma “Fuskantar Kalubalen Ƙarya, Na’urar AI, da Gibin Amincewa a Jarida.”

Sauran muhimman batutuwa sun haɗa da alaƙar jarida da tsaro, da kuma hanyoyin samun jari ga editoci bayan aikin jarida.

Kungiyar ta ce fiye da ‘yan jarida 500 daga Najeriya da ƙasashen waje za su halarci taron, wanda shi ne karo na biyu da aka shirya shi a Abuja cikin shekaru 12.

Kungiyar NGE ta bayyana cewa taron na bana zai samar da dandalin da editoci za su tattauna kan yadda za su inganta ci gaban ƙasa da haɗa kan jama’a ta hanyar jarida mai gaskiya da alhakin gudanarwa.

NAN.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here