Mamallakin jaridar PRNigeria ya kai NIPSS ƙara kan janye shi daga samun horon SEC 47 ba bisa ka’ida ba

NIPSS 1

Mamallakin jaridar PRNigeria Malam Yushau A. Shuaib, ya shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan janye shi daga shirin samun horo na babban darasin kan harkokin Gudanarwa (SEC) 47 na cibiyar nazarin siyasa da dabaru ta ƙasa (NIPSS) da ke Kuru, a Jihar Filato.

A cikin ƙarar da aka yi wa kwanan wata THC/ABJ/CS/1329/2025, Shuaib, ƙwararren masani a fannin hulɗar jama’a, yana neman diyyar Naira biliyan ɗaya saboda raɗaɗin zuciya da ɓata masa suna, tare da ƙarin Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin shari’a.

Ya ce tun a ranar 16 ga Yuni, 2025 ya aika da sanarwar gaban-shari’a ga daraktan NIPSS, Farfesa Ayo Omotayo, amma ba a bi ta ba.

Lauyansa, babban lauya (SAN) Yunus Abdulsalam, ya nemi kotu ta soke janyewar Shuaib daga SEC 47 tare da dawo da shi da dukkan hakkoki da fa’idodi.

Shuaib ya kuma nemi kotu ta hana NIPSS da jami’anta daga ci gaba da tsangwama, barazana ko cin zarafi ta hanyar internet.

Karin labari: Babbar Jojin Najeriya za ta rantsar da sababbin lauyoyi masu muƙamin SANs a ranar 29 ga Satumba

A cikin hujjojin da ya gabatar, Shuaib ya ce wallafar labarin PRNigeria ba za ta iya zama hujjar ladabtar da shi ba, kasancewar ba shi ne ya rubuta ko ya amince da shi ba.

Ya kuma yi zargin cewa NIPSS ta kutsa cikin imel ɗinsa ba tare da izini ba, abin da ya saba wa haƙƙin sirri a ƙarƙashin sashen 37 na kundin tsarin mulki.

Haka kuma ya ce ladabtar da shi saboda ra’ayin ƙwararru da aka wallafa ya sabawa haƙƙin faɗar albarkacin baki na sashen 39(1).

Shuaib ya ƙara da cewa an hana shi shiga tafiyar nazari ta ƙasashen waje duk da cewa ya biya kuɗin shiga shirin Naira miliyan 18.3 gaba ɗaya, inda ya bayyana wannan a matsayin wariya da karya yarjejeniya.

Ya kuma ce an janye shi daga shirin bisa zargi, ba tare da an ba shi damar kare kansa ba, abin da ya ce ya sabawa haƙƙin samun adalci a ƙarƙashin sashen 36(1).

A cikin takardar da ta ƙunshi sakin layi 40, Shuaib ya nuna cewa an zaɓe shi daga kungiyar kwararru kan harkokin yaɗa labarai (NIPR) domin wakiltar ƙungiyar a SEC 47, kuma shugaban ƙasa ya amince da wannan zaɓen.

Ya gabatar da wasiƙar karɓuwa, shaidar biyan kuɗi da kuma bin ƙa’idodin makarantar NIPSS, amma duk da haka, ya ce an ci gaba da tsangwama da gagarumin ladabtarwa a kansa.

Ya bayyana cewa tun daga watan Maris, 2025 aka fara aika masa da takardar tambaya kan wani labari da PRNigeria ta wallafa, sannan daga baya aka sake tsawata masa kan wani imel ɗin da bai kai ga wallafa ba.

A cewarsa, duk waɗannan ba su da tushe a cikin dokokin ladabtarwa na NIPSS, har ila yau, ya ce takardar janye shi daga SEC 47 wacce aka rubuta a ranar 2 ga Yuni, 2025 an aika ta ne kawai ga NIPR, ba tare da an mika masa kai tsaye ba.

Shuaib na neman kotu ta dawo da shi cikin shirin SEC 47, tare da bayyana cewa NIPSS ba ta da hurumin hukunta shi saboda labarin wata kafar jarida mai zaman kanta.

Ya kuma nemi kotu ta tabbatar da cewa kutse cikin imel ɗinsa ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma ayyana janyewarsa a matsayin ba bisa ka’ida ba, rashin adalci da nuna bambanci.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ce har yanzu babban alkalin babbar kotun tarayya, Mai Shari’a John Tsoho, bai saka ranar sauraron ƙarar ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here