Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Nuhu Anka ya fitar, ya bayyana cewa matakin sauya sheƙar ya biyo bayan tuntubar shugabannin jam’iyya, dattawa da magoya baya a fadin jihar.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara da iyalan jam’iyyar PDP a jihar na sanar da al’umma wani muhimmin ci gaban siyasa da ya biyo bayan tuntuba mai yawa da masu ruwa da tsaki, shugabannin siyasa, dattawa da magoya baya a fadin jihar.
Bayan yin la’akari sosai, tare da la’akari da muhimmancin tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da kuma dorewar bunkasar jihar Zamfara, gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
A cewar Anka, matakin da gwamnan ya dauka ya samu tasiri ne daga kalubalen cikin gida da jam’iyyar PDP ke fuskanta a matakin kasa da na jihohi.
Sanarwar ta kara da cewa wadannan matsaloli sun hada da rikicin cikin gida da ya dade yana faruwa, sabanin ra’ayi tsakanin shugabanni da kuma matsalolin tsari da ba a warware ba a cikin jam’iyyar PDP a matakin kasa da na jiha.
Ya kuma bayyana cewa wadannan matsaloli sun ci gaba da haifar da rashin tabbas da kuma abubuwan da ke dauke hankali wanda ka iya hana gudanar da mulki yadda ya kamata da kuma isar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar Zamfara.
Anka ya kara jaddada cewa gwamnan na ci gaba da jajircewa wajen magance matsalolin tsaro da ci gaban jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa ya zama dole gwamnan ya hada kai da wata jam’iyya ta siyasa da za ta samar da karin hadin kai, kwanciyar hankali da kuma ingantacciyar hadin gwiwa da gwamnatin tarayya domin amfanin al’ummar jihar Zamfara.
Sanarwar ta kara da cewa an gudanar da tattaunawar karshe da ta kai ga wannan muhimmin mataki a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau karkashin jagorancin mataimakin gwamna tare da manyan jami’an gwamnati da kuma manyan masu ruwa da tsaki na siyasa.
Haka kuma gwamnan ya nuna godiyarsa ga mambobin jam’iyyar PDP saboda goyon bayan da suka ba shi tsawon shekaru, inda ya bayyana cewa halin da siyasar ke ciki a yanzu ne ya sanya daukar wannan mataki ya zama dole.
Sanarwar ta kara da cewa ta hanyar shiga jam’iyyar APC, gwamnan ya sake jaddada kudurinsa na karfafa hadin kai, inganta tsaro, hanzarta ci gaba da kuma tabbatar da cewa jihar Zamfara ta amfana daga karuwar hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.
Dauda Lawal na cikin gwamnonin da ake sa ran za su nemi sake tsayawa takara a babban zaben shekarar 2027.













































