Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Litinin ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke wanda ya hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan, jihar Oyo, ba tare da bai wa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido damar shiga takarar shugabancin jam’iyyar ba.
A hukunci daya tilo da kwamitin alkalai uku na kotun daukaka kara ya yanke, kotun ta amince da hukuncin da mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar 14 ga watan Nuwamba, wanda ya umarci jam’iyyar ta bai wa Lamido damar shiga takarar shugabancin jam’iyyar na kasa.
Karanta: Sabon labari: Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da ya hana INEC amincewa da taron PDP
Kotun daukaka kara ta bayyana cewa matakin da jam’iyyar PDP ta dauka na ci gaba da gudanar da taron duk da umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar na dakatar da shi ya nuna rashin girmama kotu tare da raina ikon kotu.
A cewar kwamitin alkalai, babu wata gardama cewa jam’iyyar ta gudanar da taron duk da umarnin kotu da ya umurce ta ta bai wa Lamido damar shiga cikin taron da kuma takarar shugabancin jam’iyyar.
Kotun ta yi watsi da hujjar da jam’iyyar PDP ta gabatar cewa ta gudanar da taron ne bisa bin hukuncin wata kotu da take da daidai ikon shari’a.
Kotun ta ce ba hakkin wani bangare a cikin shari’a ba ne ya zabi wane umarnin kotu zai bi ko kuma wanda zai yi watsi da shi.
Kotun ta kara da cewa abin da ya kamata jam’iyyar PDP ta yi shi ne neman dakatar da aiwatar da hukuncin ko kuma ta daukaka kara kan hukuncin da aka yanke.
Saboda haka kotun ta tabbatar cewa kotun da ta fara sauraron shari’ar ta yi daidai da ta karbi karar Lamido tare da amincewa da bukatun da ya gabatar.
Kotun daukaka kara ta yi watsi da daukaka karar da aka yi mai lamba CA/ABJ/1695/2025 bisa rashin ingantaccen dalili, sannan ta umurci jam’iyyar PDP ta biya tarar Naira Miliyan Biyu.













































