Bankin raya ayyukan Noma da IOM sun kafa asusun dala miliyan 200 don tallafa wa ‘yan Najeriya da suka rasa muhallansu

Screenshot 20251025 125633 750x430

Bankin raya ayyukan Noma (BOA) tare da ƙungiyar tabbatar da dawo da ƴan gudun hijira kasashen su (IOM) sun kafa wani asusu na dala miliyan 200 domin tallafa wa ‘yan Najeriya da suka rasa muhallansu da kuma ƙarfafa haɗin kan tattalin arziƙi.

A cewar bankin, wannan haɗin gwiwa na nufin samar da damar dogaro da kai ga fiye da mutane miliyan 3.8 da ke cikin sansanonin ‘yan gudun hijira a fadin ƙasar, inda zai wuce iya taimako kawai ya zama wata hanya ta dorewar ci gaba.

Bankin ya bayyana cewa, wannan asusu zai samar da tallafin kuɗin noma, horar da al’ummomin da aka raba da muhallansu, tare da haɗa manoma da kasuwanni domin ƙara ƙarfin tattalin arziƙin yankunansu.

Manajan daraktan bankin, Ayo Sotinrin, ya ce wannan haɗin gwiwa ba wai batun kuɗi kaɗai ba ne, illa dai zuba jari a cikin mutane da kuma zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.

Wani bayani daga mataimakin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin sadarwa, Dada Olusegun, ya bayyana cewa an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Abuja tsakanin Ugochi Daniels, mataimakiyar daraktar gudanarwa ta IOM, da Sotinrin na BOA.

Wannan mataki ya biyo bayan alkawarin da gwamnatin tarayya ta ɗauka watanni huɗu da suka wuce na ware naira biliyan 200 don tallafa wa harkokin noma da kuma naira tiriliyan 1.5 don ƙarfafa jarin Bankin kula da ayyukan Noma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here