Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci sarakunan jihar da su ci gaba da gudanar da bukukuwan hawa doki na gargajiya domin karewa da kuma raya al’adun Kano mai dogon tarihi.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Asabar, inda ya ce gwamnan ya bayar da umarnin ne a lokacin bikin Kanfest (Kalankuwa) na bana da aka shirya domin baje kolin al’adun Kano.
Yusuf ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa masarautu domin tabbatar da cewa wannan al’ada ta hawa doki wadda ta shahara a duniya ta ci gaba da bunƙasa, tare da tabbatar da cewa tana zama abin alfahari ga al’ummar Kano.
Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta zuba jari a fannonin fasaha, al’adu da yawon buɗe ido, domin haɗa kan jama’a, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Mai martaba Sarkin Kano kuma shugaban majalisar sarakunan jihar, Malam
Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa Gwamna Yusuf bisa wannan hangen nesa na farfaɗo da al’adun gargajiya na Kano.
Bikin Kalankuwa na bana ya gudana na tsawon kwanaki uku, inda aka nuna kayayyakin gargajiya, abinci na gida, wasanni, rawa, zane, tukwane da sauran nune-nune da suka jawo hankalin masu kallo daga ciki da wajen Najeriya.
NAN













































