Najeriya na shirin sake bude ofishin jakadancinta a Koriya ta Arewa

Nigerian embassy in North Korea 1.jpeg

Najeriya na shirin sake bude ofishin jakadancinta a Pyongyang, babban birnin kasar Koriya ta Arewa, bayan rufe shi a farkon shekarar 2021 sakamakon annobar COVID-19.

Patrick Imologhome, jami’in hulda da jama’a na Najeriya a Koriya ta Arewa, ya bayyana shirin a wata ganawa da Aleksandr Matsegora, jakadan kasar Rasha a kasar Asiya, a ranar 11 ga watan Disamba, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin jakadancin Rasha ta bayyana.

Sanarwar ta ce dukkanin jakadun biyu sun yi musayar ra’ayi sosai kan batutuwan da suka shafi Koriya.
Matsegora ya kuma bayyana fatan alheri ga nasarar aiwatar da tsare-tsare na maido da ofishin diflomasiyyar Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here