An kashe kwamandan rundunar soja yayin da Boko Haram suka kai hari wani sansanin soja a Borno

Boko Haram 750x430

An kashe wani kwamandan rundunar sojojin Najeriya bayan da ake zargin mayakan ISWAP sun kai hari wani sansanin soja da ke Kukawa a jihar Borno.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, a cewar Zagazola Makama, wata kafar wallafa labarai da ke mayar da hankali kan yaki da masu tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi, harin ya yi sanadiyyar asarar rayuka daga bangarorin biyu tare da sa sojoji shiga musayar wuta na tsawon lokaci.

Majiyoyi sun shaida wa Makama cewa an gano tabon jini a wajen sansanin, wanda ke nuna cewa wasu daga cikin masu tayar da kayar baya sun jikkata ko sun mutu yayin arangamar.

Wata majiya daga garin ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai harin ne a sansanin sojin da misalin karfe 12:30 na dare a ranar Litinin.

Majiyar ta kara da cewa ‘yan ta’addan sun shiga garin daga bangarori daban-daban tare da kai hari sansanin sojin.

Wata majiya daga bangaren tsaro ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun fatattaki sojojin daga sansanin, sannan suka kona wasu motoci tare da kwashe makamai da alburusai.

Majiyar ta kuma bayyana cewa ba za ta iya bayyana adadin wadanda suka mutu ba, amma abin bakin ciki ne cewa an rasa kwamandan rundunar a harin.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a watan da ya gabata ma ‘yan ta’addan sun kai hari sansanin sojin amma jaruman sojojin sun dakile harin tare da kashe ‘yan ta’adda da dama.

Rahoton ya kuma nuna cewa an yaba wa jaruntakar sojojin daga al’ummar yankin, inda aka yabawa kwamandan rundunar sosai musamman a kafafen sada zumunta.

Rahoton ya kara bayyana cewa sojoji sun kama wani dan Boko Haram da ya jikkata a cikin al’umma yayin da ake kokarin kai shi sansanin soji.

Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya yi yunkurin tserewa, lamarin da ya haddasa sake barkewar harbe-harbe.

Majiyoyi sun ce halin da ake ciki yana karkashin kulawa, inda sojoji ke ci gaba da tsaron yankin tare da gudanar da karin ayyuka domin gano sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.

Sabon harin ya faru kusan mako guda bayan da ake zargin mayakan Boko Haram da ISWAP sun yi yunkurin kai hari wuraren sojoji a Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa sama da ‘yan ta’adda 50 da ake zargi an kashe su a hare-haren jiragen yaki a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here