An gudanar da addu’ar kwana uku ga marigayi Sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo, Alhaji Idris Adamu Dankabo, a ranar Lahadi a Kano.
Malam Umar Ali tare da wasu malamai sun jagoranci addu’ar, inda aka yi karatun Alƙur’ani domin neman rahamar Allah ga marigayin, mahaifinsa da mahaifiyarsa.
Dubban jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar sun halarci taron, wanda aka gudanar a gidan kakansa, marigayi Alhaji Adamu Dankabo. Fitattun mutane da dama sun halarta ciki har da tsohon Ministan Shari’a, Bello Adoke; Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano; mataimakinsa, Aminu Gwarzo; da mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai, Abdul’Aziz Abdul’Aziz.
Haka kuma, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, attajirin ɗan kasuwa Alhaji Aliko Dangote, da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Rurum, sun kasance cikin mahalarta addu’ar.
Labari mai alaƙa: Hakimin Kabo Alhaji Idris Adamu Dankabo, ya rasu
Marigayi Idris Dankabo, mai shekaru 48, ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a cikin birnin Kano da dare a ranar Alhamis.
Jana’izarsa ta gudana a ranar Juma’a a fadar Sarkin Kano, Kofar Kudu, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, tare da taron jama’a mai yawa.
Dankabo shi ne ɗa na fari ga marigayi Alhaji Adamu Dankabo, wanda ya kasance Jarma na Kano kuma wanda ya kafa tsohon kamfanin jiragen sama na Kabo Air.
Dangin Dankabo ana ɗaukar su a matsayin manyan iyalai masu tasiri a Kano, inda marigayi Adamu Dankabo ya shahara wajen kasuwanci, siyasa da aikin alheri.
Kamfanin Kabo Air, wanda aka kafa a shekarar 1980, ya yi aiki da jiragen cikin gida da ƙasashen waje kafin daga baya ya mayar da hankali kan jigilar Alhazai da kuma ayyukan haya.
Matsayin marigayi Idris Dankabo a matsayin Sarkin Gabas na Kano na daga cikin manyan mukaman gargajiya a masarautar Kano, tare da nauyin al’adu da na gudanarwa.
Rasuwarsa a cikin wannan ƙuruciya ta bar gibi mai girma a tsarin shugabancin gargajiya na masarautar Kano.













































