Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta kama wata hodar ibilis da ke ƙunshe cikin wasu littattafn addini da aka so yin safararta zuwa ƙasar Saudiyya.
Cikin sanarwar nasarorin mako-mako na hukumar da kakakinta, Femi Babafemi ya aike wa BBC ya ce hodar, ƙulli 20 mai nauyin giram 500 an shirya ta cikin shafukan littattafan da nufin safararta zuwa ƙasar ta Saudiyya.
Ya ce jami’an hukumar ne suka yi nasarar gano hodar ranar 15 ga watan Afrilu a maɗaukan kaya na wani kamfani da ke shirin fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.
Babafemi ya ce, hukumar ta kuma gano wata tabar wiwi cikin wani maɗauki da aka shigar da shi ƙasar daga Amurka.
Hukumar ta kuma kama wani matashi, mai shekara 22 a kan hanyar zuwa Bichi da ke jihar Kano da kwalaben allurar pentazocine 277, manne da silatif a cinyoyinsa da al’aurarsa.