Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 4 a cibiyar kula da ruwa da ke Bauchi

Police badge

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da wani mummunan hatsarin ruwa wanda ya yi sanadin mutuwar ma’aikata hudu a cibiyar kula da ruwa ta Gubi da ke Bauchi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Ahmed Wakili, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Lahadi a Bauchi.

Ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin tsaftar kula da bututun rarraba ruwan a cikin ramuka na kamfanin.

Wakili ya bayyana sunayen wadanda suka mutu da suka hada da Shayibu Hamza (48), Abdulmalik Yahya (29), Jamilu Inusa (29) da Ibrahim Musa (42).

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa dukkansu mazauna kauyen Firo ne da ke karamar hukumar Ganjuwa a jihar.

Wakili ya ce ma’aikatan sun shiga na’urar ne domin yashe bututun ramin da lamarin ya faru.

Wakili, duk da haka, ya jaddada mahimmancin tsauraran matakan tsaro a cikin irin wadannan mahalli masu haɗari, inda ya bukaci ma’aikata a irin wannan aiki da su bi ka’idojin tsaro da aka kafa.

Wakili ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Sani-Omolori Aliyu, ya mika sakon ta’aziyya a madadin hukumar ga iyalan mamatan, abokan aikinsu da kuma hukumomin kamfanin.

Ya sake jaddada kudirin ‘yan sanda na inganta matakan tsaro don hana afkuwar irin haka nan gaba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here