Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da bukatar daukacin al’ummar jihar Kano ta hanyar canza sunan jami’ar ilimi ta tarayya da ke Kano zuwa jami’ar ilimi ta Maitama Sule.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa shugaban kasar, ta hanyar wata sanarwar manema labarai da fadar shugaban kasa ta fitar dauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da sauya sunan jami’ar da sunan marigayi Maitama Sule, daya daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa daga yankin arewacin kasar nan.
‘’Maitama Sule, Danmasanin Kano, ya kasance jami’in diflomasiyya, dan siyasa, kuma dattijo wanda ya rasu a shekarar 2017 yana da shekaru 88. Ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban zamantakewa da siyasar kasa”.
Labari mai alaƙa: Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Kano zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na internet ranar Litinin.
A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta sauya sunan jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano zuwa tsohon suna ta na Jami’ar Northwest.
‘’ Matakin da gwamnatin jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP ta dauka na sauya sunan jami’ar mallakar gwamnati ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar Kano. Don haka na dauki nauyin kudirin dokar canza sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano da sunan marigayi Danmasanin Kano.