Rundunar ‘yan sanda a jihar Kebbi ta tabbatar da kashe mutane 11 a wani hari da wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka ka yi a wasu kauyukan karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Litinin.
Abubakar ya ce: “A ranar 09/03/2025 da misalin karfe 20: 47 wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi dauke da makami da manyan muggan makamai suka mamaye kauyukan Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Birnin Debi, Garin Nagoro da Garin Rugga.
“Dukkan su suna a karamar hukumar Arewa kuma al’ummomin kan iyaka ne tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Sanarwar ta kara da cewa da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Bello Sani, ya garzaya wajen da lamarin ya faru domin tantancewa nan take.
(NAN)