Sarkin Zuru Manjo Janar Muhammadu Sami II mai ritaya ya rasu yana da shekara 81 da haihuwa.
Sakataren yaɗa labarai na gwamantin jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa sarkin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan ranar Asabar da dare.
Sarkin tsohon gwamnan mulkin soja ne na jihar Bauchi lokacin mulkin marigayi Janar Muhammadu Buhari a 1984 zuwa 1985.
Sanarwar ta ce Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya siffanta marigayin a matsayin “uban ƙasa mai cike da hikima kuma wanda ya sanya hidimar al’ummarsa a gaba”.
Sarkin ya rasu ya bar mata huɗu da ‘ya’ya bakwai.













































