INEC ta ayyana zaben cike gurbi na jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba

INEC CVR

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana zaben cike gurbi na mazabar Kaura-Namoda ta Kudu na dan majalisar dokokin jihar Zamfara a matsayin wanda bai kammalu ba sakamakon kura-kuran da aka samu a rumfunan zabe biyar.

Da yake bayyana sakamakon zaben da misalin karfe 1:30 na safe, jami’in kula da masu kada kuri’a, Farfesa Lawal Sa’adu na jami’ar tarayya ta Gusau, ya bayyana rashin bin ka’ida a unguwannin Sakajiki da Kyambarawa a matsayin dalilin yanke hukuncin.

A cewar Farfesa Sa’adu, tazarar shugabanci tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu wato APC da PDP ya kai kuri’u 1,662, wanda bai kai adadin katinan zabe na dindindin (PVC) da aka karba a rumfunan zabe da abin ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here