Kano: An dakatar da Alkalan kotu 4 da Magatakarda kan wasu laifuka

Dije, Aboki, Kano, dakatar, Alkalan, kotu, Magatakarda, wasu, laifuka
Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa a kan wasu alkalai hudu da kuma magatakardar kotu daya bisa wasu laifuka...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa a kan wasu alkalai hudu da kuma magatakardar kotu daya bisa wasu laifuka.

SolaceBase ta rawaito cewa an dauki matakin sanyawa jami’an shari’a takunkumi a Hukumar Ma’aikatar Shari’a ta Jiha yayin taronta na 72 da aka gudanar a ranar 11 ga watan Yuni 2024.

Hakazalika, hukumar ta kuma a taronta na 73 da ta gudanar a ranar 20 ga watan Yunin 2024, ta tattauna kan kararrakin da ta samu a gaban kotun Majistare ta 60 da Tijjani Saleh Minjibir ya jagoranta.

Karin labari: Surukar mataimakin shugaban kasar Najeriya ta rasu

Ya ce ba a gamsu da amsoshin tambayoyin da aka bayar ba.

Hukumar ta ce tana kallon abin da babban alkalin kotun ya yi a matsayin babban rashin da’a da rashin ko in kula na shari’a tare da daukar matakin dakatar da Tijjani Saleh Minjibir daga aikin shari’a na tsawon shekara daya nan take.

Karin labari: Rikicin Masarautar Kano: Kotu Ta Dage Shari’ar Na Sa’o’i Kadan

Ya dakatar da duk wasu ayyukan shari’a kuma ya kai rahoto ga hedkwatar babban kotun don aikawa.

Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya fitar a ranar Litinin, ta ce matakin ladabtar da Alkalan Kotun Majistare din ya hada da Talatu Makama ta kotun majistire mai lamba 29, da babbar majistire Rabi Abdulkadir da ke kotun majistire mai lamba 48 da kuma babban magatakarda Abdu Nasir na sashin daukaka kara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here