Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya rasa surukarsa, Maryam Abubakar-Albishir, mai shekaru 69, wacce ta rasu a Kano da yammacin Lahadi bayan doguwar jinya.
Kakakin mataimakin shugaban kasar, Mista Stanley Nkwocha, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Litinin a Abuja.
Nkwocha ya ce za a yi jana’izar marigayiyar wadda ita ce mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa, Misis Nana Shettima, ranar Litinin da yamma a Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Karin labari: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Bada Umarnin Rushe Gidan Sarki Na Nasarawa
Ya ce marigayiyar an san ta a matsayin uwa mai koyi da kirki a cikin al’ummarta sannan kuma musulma ce.
Nkwocha,” Ana mutunta ta saboda hikimarta, tausayinta, da sadaukarwarta ga ayyukan agaji.
Karin labari: Hukuncin da kotu ta yanke game da shari’a kan sarautar Kano
“Da yawa suna tunawa da ita a matsayin tushen jagora da tallafi, a cikin danginta da sauran al’ummar Kano.
“Al’umma na mika ta’aziyyarta ga mataimakin shugaban kasa Shettima, da Misis Nana Shettima, da iyalansu a wannan lokaci.”