Sojoji sun ceto mutane 7 da aka yi garkuwa da su a Kano

IMG 20251130 WA0082 750x430

Dakarun rundunar soji ta Operation MESA Bataliya ta Uku ta ceto mutane Bakwai da masu garkuwa da su suka sace a yankamaye cikin gari da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na bataliya ta Uku, Kaftin Babatunde Zubairu, ya fitar a ranar Lahadi ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren 29 ga Nuwamba da misalin ƙarfe 11 na dare.

Kaftin Zubairu ya ce bayan samun kiran gaggawa kan harin da gungun ’yan bindiga suka kai a ƙafa inda suka yi awon gaba da mutum goma tare da kashe wata mata mai shekaru sittin, rundunar sojoji da jami’an ’yan sanda suka isa wurin cikin gaggawa suka bi sahun maharan zuwa hanyar Rimaye.

Sojojin sun yi musayar wuta da maharan cikin ƙarfi wanda hakan ya ba su damar kubutar da mutane bakwai daga cikin waɗanda aka sace.

Ƴan bindigar sun arce zuwa ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina, kuma ana ci gaba da bin diddigin su domin gano inda suke.

Kwamandan Bataliya ta Uku ya yaba wa sojojin bisa jarumtaka da ƙwarewa da suka nuna a aikin, tare da ƙarfafa al’ummar jihar su rika ba da sahihan bayanai cikin lokaci ga hukumomin tsaro don taimaka wa ci gaba da ayyukan tabbatar da tsaro.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here