Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ceci rayuka 101 da kadarorin da darajarsu ta kai Naira miliyan 21, yayin gobara 21 da suka auku a jihar cikin watan Satumba.
Cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce cikin watan na Satumba, hukumar ta samu kiran gaggawa 77 da kiran kuskure 11 a cibiyoyinta 27.
Ya kara da cewa, an yi rashin mutane 8, yayin da aka yi asarar kadarorin da darajarsu ta kai Naira miliyan 7.3 a wancan lokaci.
Saminu Abdullahi ya kuma alakanta galibin gobarar dake aukuwa a jihar da rashin kula da gas na girki da amfani da kayayyakin wuta marasa inganci.
Yana mai shawartar mazauna su rika lura yayin da suke amfani da wuta domin kare aukuwar gobara.
Har ila yau, kakakin ya shawarci iyaye su rika sa ido kan zirga-zirgar ‘ya’yansu da kuma hana su iyo ba tare da wani jagora ba.
NAN












































