Gwamnatin Kano ta musanta cewa EFCC ta kama uwagidan Gwamna Ganduje

Ganduje sad
Ganduje sad

Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahotannin dake cewa, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu’annuti, ta kama Hajiya Hafsat, uwargidan Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya fitar, ta bayyana takaici, game da yadda aka gaza alakanta labarin mara tushe da sahihiyar majiya kamar ta EFCC da aka ce ta yi kamen.

Har ila yau, ya bayyana takaicin yadda labarin ke wadari a kafafen sada zumunta ba tare da an tabbatar da sahihancinsa daga gwamnatn jihar ko hukumar ta EFCC ba.

Rahotannin kafafen yada labarai sun bayyana cewa, hukumar EFCC ta yi wa uwargidan Gwamnan tambayoyi a jiya Litinin, biyo bayan korafin da dan gwamnan, AbdulAzeez Ganduje ya gabatar dangane da badakalar fili.

Tun da farko, EFCC ta gayyaci uwargidan Gwamnan ta bayyana a hedkwatarta dake Abuja a ranar 13 ga watan Satumba. Amma kuma ta gaza yin hakan, inda hukumar ta yi barazanar kamata. Majiyoyi makusantanta sun bayyana cewa, ta yi bulaguro zuwa Birtaniya domin halartar bikin kammala karatun danta a wancan lokaci.

Malam Garba dai ya ce ba a tsare ko kama uwargidan ba, kuma yanzu haka tana gudanar da harkokinta kamar yadda ta saba.

Ya kuma yi kira ga jama’ar Kano su yi watsi da jita-jitar, tare da kwantar da hankalinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here