Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da korar Engr. Mu’azu Magaji, da aka fi sani da Ɗan Sarauniya daga muƙaminsa na shugaban kwamitin jihar mai kula da aikin shimfida bututun gas tsakanin Ajaokuta da Kaduna da Kano watau AKK.
Rahoton Solacebase ya bayyana cewa, korar ta biyo bayan rashin tabuka abun kirki daga shugaban na kwamitin.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya fitar.
Idan za a iya tunawa, gwamna Ganduje ya taba korar Engr. Magaji daga mukamin kwaminishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar a cikin watan Afrilun 2020, saboda murnar da ya yi da mutuwar tsohon shugaban ma’aikatan shugaban kasa wato marigayi Abba Kyari, a kafafen sada zumunta.
Daga baya kuma, ya sake nada shi a matsayin shugaban kwamitin kula da aikin shimfida bututun gas na AKK a watan Afrilun bana.
Sanarwar ta ce Engr. Magaji ya gaza, wajen sauke nauyin da aka dora masa na jagorantar aikin da gwamnatin ke ba matukar muhimmanci.
Ta kara da cewa, an bukaci korarren shugaban da ya mika dukkan harkokin kwamitin ga mataimakinsa Aminu Babba Dan Agundi, Sarkin Dawaki Babba. Haka kuma gwamnan Ganduje na gode masa tare da yi masa fatan alkhairi.













































