Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Karin Sunayen Ministoci

BREAKING 750x430
BREAKING 750x430

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika karin sunayen mutanen da yake son nadawa ministoci ga Majalisar Dattawa.

Tinubu ya aike wa majalisar sunayen ne a yayin da take tsaka da tantance karashen mutane 28 da ya aike mata da farko a ranar Laraba.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya mika sunayen ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio.

A makon jiya ne Tinubu ya mika wa majalisar sunayen rukunin farko na mutanen da yake son nadawa ministoci daga 25 daga cikin jihohi 36 da birnin tarayya da ke kasar.

Mutanen da ya fara bayarwa sun hada da mata bakwai da maza 21, wadanda cikinsu kuma akwai tsoffin gwamnoni hudu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here