Gwamnan Kano ya kaddamar da shirin horar da Jami’an tsaro 2,500

Abba Kabir Yusuf 750x430
Abba Kabir Yusuf 750x430
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir ya bayyana kwarin gwiwarsa akan hukuncin da kotun koli za ta yanke kan karar zaben gwamnan Kano.

Gwamnan ya bayyna hakan ne yayin bikin kaddamar sabbin jami’an bayar da tsaro ga ma’aikatun gwamnati da kanfanoni na Jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf Kano Governor, Gwamnan

Jami’an su 2,500 da aka yaye a makarantar horar da matasa, a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata.

“Muna da yakinin cewa alkalan kotun koli za su yi adalci wajen daukaka karar da ke gabansu, don haka jama’ar Kano su kwantar da hankalinsu,” inji Abba.

Karanta wannan: Cikin hotuna: mataimakin shugaban kasa da gwamnoni sun halarci auren Dan Abacha

Ya bayyana cewa an kafa makarantar horar da jami’an tsaro a zamanin gwamnatin Rabi’u Kwankwaso da nufin horar da matasa kan harkokin tsaro.

“An zabo wadanda aka horar ne daga kananan hukumomi 44, kuma za a dauke su aiki tare da tura su ga hukumomi da ma’aikatun gwamnati bayan kammala horon.

“Gwamnatinmu ce ta kafa wannan makarantar horarwa a shekarar 2011 kuma an horar da matasa aikin tsaro da tura su zuwa ma’aikatu da hukumomi daban-daban na jihar.

“A yau, muna kaddamar da wannan shirin tare da jami’ai 2,500 wadanda dukkansu za a koya musu dabarun tsaro.”

Karanta wannan: Malamai 3 ne kacal a Makarantar Sakandiren yaran mu Mata-Iyaye a Sumaila

Yusuf ya yaba da goyon bayan da mazauna Kano suke ba su, ya kuma bukace su da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda da kuma son zaman lafiya.

“Ina so in tabbatar wa al’ummar jihar nan cewa gwamnatina za ta ci gaba da samar da shirye-shiryen ci gaban Dan Adam da za su tallafawa matasan Kano.

Karanta wannan: An saki Emefiele daga gidan yarin Kuje bayan cika sharuddan beli

A cewar sa, wadanda suka ci gajiyar shirin za a samar musu da ayyukan yi hukumomi da ma’aikatu na jiha da kuma kananan hukumomi 44.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here