Kirsimeti: Lokacin tunawa da marasa karfi da marasa lafiya-kungiyar ACF

ACF
ACF

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, Wazirin Dutse, ya taya mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu.

Alhaji Bashir Dalhatu, a wani sako da ya aike a ranar Asabar, ya bukaci mabiya addinin kirista da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’in samun hadin kai da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Ya yi kira ga Kiristoci da su sadaukar da kansu ga hidimar al’umma daidai da koyarwa ta gaskiya wadda ta yi nuni da hakuri, kyautatawa, taimakawa mabukata, da nuna kauna ga juna.

Kungiyar ACF

Karanta wannan: Gwamnan Kano ya kaddamar da shirin horar da Jami’an tsaro 2,500

Shugaban Kwamitin Amintattu na ACF ya bukaci daukacin mabiya addinin kirista a Najeriya da su yi amfani da lokacin bukukuwa domin yin addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban kasa.

Karanta wannan: Cikin hotuna: mataimakin shugaban kasa da gwamnoni sun halarci auren Dan Abacha

Alhaji Bashir Dalhatu ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rinka kokarin wanzar da zaman lafiya a cikin rayuwar yau da kullum.

Kazalika, ya ja hankalin masu hannu da shuni da su rika tunawa da mabukata da marasa galihu a cikin al’umma, yana mai cewa lallai wannan zamani yana da matukar wahala.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here