Kwalejin fasaha ta jihar Kano za ta fara kwasa-kwasai ta kafar Internet

Kano Poly new
Kano Poly new

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara gudanar da darusa ta kafar Interner, ta yadda za ta yi gogayya da takwarorinta na sassan duniya.

Shugaban kwalejin Dakta Abubakar Umar Farouk ne ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar ICAN reshen jihar Kano makon jiya a ofishin sa.

“Nan ba da jimawa ba za mu fara shirye-shirye ta kafar Internet a Kano Polytechnic domin malaman mu su fara gabatar da laccoci ta kafar internet”.

ICAN 1, Fasaha

Farouk ya kara da cewa tuni kwalejin ta fara sake fasalin wasu shirye-shiryenta domin samar da ayyukan yi ga wadanda suka kammala karatu.

Karanta wannan: Kirsimeti: Lokacin tunawa da marasa karfi da marasa lafiya-kungiyar ACF

Tun da farko shugaban kungiyar ICAN shiyyar Kano Malam Habibu Ayuba, ya ce ba bu wata al’umma da za ta kai ga gaci ba tare da gudunmawar ‘yan ICAN ba.

ICAN 2, Fasaha

Ayuba, ya taya murna ga sabon shugaban kwalejin wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar ICAN reshen jihar Kano.

“Mun yi farin ciki da zabar Dakta Abubakar Umar Farouk a matsayin shugaban kwalejin kimiyya da fasaha, sanin kowa ne ba’a yi zaben tumun dare ba, domin zai bada gudunmawa sosai ta yadda kwalejin zata kai ga wani matsayi mai girma.”

Karanta wannan: Gwamnan Kano ya kaddamar da shirin horar da Jami’an tsaro 2,500

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya nada Dakta Abubakar Umar Farouk a matsayin shugaban kwalejin a ranar 4 ga Disambar 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here