Gwamnatin Tarayya ta fara biyan albashin malaman Jami’o’i da aka hana

Gwanatin Tarayya, Malamai, Jami'o'i, ASUU, albashi
Gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin malaman jami’o’i da aka hana a karkashin kungiyar malaman jami’o’i ASUU. Majiyoyi da dama a bangaren ilimi sun...

Gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin malaman jami’o’i da aka hana a karkashin kungiyar malaman jami’o’i ASUU.

Majiyoyi da dama a bangaren ilimi sun tabbatarwa da wakilinmu a Abuja faruwar lamarin a ranar Litinin.

Shugaban ASUU na Jami’ar Bayero ta Kano BUK, Farfesa Ibrahim Tajo ya tabbatarwa SOLACEBASE wannan ci gaban a ranar Litinin.

Karanta wannan: Ana zanga-zangar tsadar rayuwa a Ibadan

Farfesa Tajo ya ce yawancin malamai suna karbar kudin.

“Eh, an fara biyan kudin ne a karshen mako yayin da wasunmu suka karbi kudin a daren ranar Asabar, in ji Farfesa Tajo.

”An biya albashin da ba’a biya ba a cikin watanni takwas da aka hana.”

“Muna fatan za’a aiwatar da sauran biyan.”

Karanta wannan: Sojojin ruwan Maroko sun ceto baƙin haure ƴan Afirka 141

A watan Oktobar shekarar 2023 da ta gaba ne shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sakin hudu daga cikin watanni takwas na ASUU da ta hana ma’aikata albashi.

An hana biyan albashin ne a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan wasu kungiyoyin jami’o’i da suka fara yajin aikin da ya kwashe watanni takwas ana yi a shekarar 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here